Majiyoyin labarai a HKI sun bayyana cewa tsoron tsoron maida martanin JMI kan HKI saboda hare haren da ta kai kan ofishin jakadancin kasar a birnin Damascus na kasar siriya ya jefa tsaro cikin bangarori daban daban na HKI ya kuma gurgunta ayyuka a can.
A ranar 1 ga watan Octonam shekara ta 2024 da muke ciki ne jiragen yakin HKI sukakai hare hare a kan karamin ofishin jakadancin kasar Iran dake birnin Damascus na kasar Siriya . Hare haren dai sun yi sanadiyyar shahadar mutane 7 daga cikin jami’an diblomasiyyar kasar Iran a yayinsa wasu 6 suka ji rauni.
Mafi yawan kasashen duniya dai sun yi allawadai da hare haren, bayan haka jami’an gwamnatin JMI sun sha alwashin daukar fansa kan HKI.