HKI Tan Tabbatar Da Cewa Hamas Da Jihadul Islamu Zasu Sami Nasarar Cilla Makamai Masu Linzami Daga Yankin yamma Da Kojin Jordan Nan Gaba

Tashar talabijin “Kan” Ta HKI ta nakalto wani kwararre a kan harkokin Falasdinawa na cewa mai yuwa nan gaba da shekara guda falasdinawa daga kungiyoyuin

Tashar talabijin “Kan” Ta HKI ta nakalto wani kwararre a kan harkokin Falasdinawa na cewa mai yuwa nan gaba da shekara guda falasdinawa daga kungiyoyuin Hamas da kuma Jihadul Islami zamu sami nasarar kera makamai masu linzami masu karfi a yankin yamma da kogin Jordan sannan su cillasu kan matsugunan yahudawa a kasar Falasdinu da aka mamaye.

Labarin ya nakalto jami’ii mai kula da al-amuran Falasdinawa na tashar ‘Kan’ mai suna Le’ur Lefi yana fadar haka ya kuma kara da cewa, maganar ita ce Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan suna iya samun makamai masu linzami masu karfi wadanda kungiyoyin biyu suke cillawa kan matsugunanan yahudawa da suke gewaye da Gaza, reshin kungiyoyin a yamma da kogin Jodan zasu sami wadanda makaman.

Lefi ya kara da cewa yana da masaniya kan cewa fasahar kera wadannan makamai sun fara shigowa yankin yamma da kogin Jordan, kuma tabbas fasahar kera makamai masu linzami masu karfi zasu isa hanun yayan wadan nan kungiyoyi a yankin nan da kimani shekara guda.

Kafin haka dai Abu Hamza mai Magana da yawan saraya Kudus na kungiyar Jihadul Islami a yankin yamma da kogin Jordan ya bada sanarwar cewa, a cikin yan kwanakin da suka gabata sun sami nasarar wargaza wasu katafaren motoci guda biyu na HKI, inda suka halaka sojojinsu da dama wadanda suka kutsa cikin sansanin yan gudun hijira na jenin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments