HKI Ta Rufe Kofar Rafah Wanda Ya Hana Fitar Da Marasa Lafiya Daga Gaza Zuwa Jinya A Waje

Majiyar kungiyar Red Crecen ta Falasdinawa ta bada sanarwan cewa a jiya Laraba HKI ta dakatar da shirin fitar da marasa lafiya da suke gaza

Majiyar kungiyar Red Crecen ta Falasdinawa ta bada sanarwan cewa a jiya Laraba HKI ta dakatar da shirin fitar da marasa lafiya da suke gaza don jinya a kasashen waje ta kofar shiga yankin da ke rafah ba tare da bada wani dalili ba.

Rashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Raed Al-Nems kakakin kungiyar kungiyar bada agaji ta Red Cresen yana fadar haka a jiya, ya kuma bayyana cewa ya sami labarin ne daga hukumar lafiya ta duniya wacce ta fara shirin fitar da Falasdinawa marasa lafiya a Gaza tun bayan da yahudawan suka bude kofar Rafa.

Yahudawan sahyoniyya sun bada wannan sanarwan ne a dai dai lokacinda suka kai mummunan hare-hare kan falasdinawa a gaza a jiyan. Labarin ya kara da cewa mai yuwa su sake bude kofar ta Rafah a yau Alhamis don ci gaba da fitar da Falasdinawa wadanda suke matukar bukatar jinya a kasashen waje. Saboda babu kayakin aikin a asbitin Al-Amal da ke Khan Yunus na yankin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted