HKI Ta Kara Hanyoyin Cutar Da Falasdinwa A Gaza Ta Hanyar Boye Boma Bomai A Mutum-mutumi

Kungiyar kare hakkin bi’adama Ta ‘The Euro-Med Human Rights Monitor’ ta bada sanarwan cewa gwamnatin HKI tana amfani da dakiyoyi a cikin mutum-mutumi ko (Bobby-Trapped)

Kungiyar kare hakkin bi’adama Ta ‘The Euro-Med Human Rights Monitor’ ta bada sanarwan cewa gwamnatin HKI tana amfani da dakiyoyi a cikin mutum-mutumi ko (Bobby-Trapped) don kara kisan Falasdinawa a areawacin Gaza.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar cewa, manufar HKI a wadan nan hare hare, itace kara kissan Falasdinawa masu yawa a arewacin gaza.

Kungiyar wace take da mazauni na din din din a birnin Geneva ta kara da cewa wannan sabon salon kashe mutanen arewacin gaza kari ne kan wadanda ta dauka a bayana, wadanda suka hada da hana shigi da abinci da magunguna, kissan kiyashi, tilastawa falasdinwa kaura daga wuri zuwa wani wurin da kuma hanasu abinci har su mutu da sauransu.

Kona tintunan Falasdinawa wadanda aka yisu da abubuwan da suke iya kamuwa da wuta na daga cikin hanyoyin da yahudawan suke amfani don kashe Falasdinawa a yankin na Gaza.

 A halin yanzu dai sojojin HKI sun ware yankin arewacin gaza, daga kudancin yankin tare da Sanya motocin yaki da tara Yashi da kasa a kan hanyoyi zuwa ko fita daga yankin. Wannan kari kan hare hare da makaman Drons da suke kaiwa kan mutanen da suka rage a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments