Gwamnatin HKI tana son budewa kanta wata jahannama a yankin yamma da kogin Jordan bayan da fara yaki gadan-gadan da kungiyoyin falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan musamman a sansanin yan gudun hjira ta Jenin.
A cikin yan kwanakin da suka gabata ne sojojin HKI suka kai wasu hare hare na musamman a wasu garuruwan a yankin yamma da kogin Jordan inda suka kashe falasdinawa da dama, sannan sun aikata ayyukan soje wadanda suka hada da rusa gine-gine da kuma hanyoyi a wadannan garuruwa.
Amma falasdinawan basu nade hannayensu suna kallon barnan da yahudawan suke yi kawai ba. Dakarun Hamas da na Jahadulislami a wadannan garuruwa sun yi kokarin kare kansu daga hare haren yahudawan, sannan sun sami nasara kashe wasu yahudawa a kusa da garin Hebron a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Wannan ya nuna cewa duk tare da tsaro mai karfi wanda sojojin yahudawan suke ganin sun samar a yankin, Falasdinawa suna iya keta su, su kuma sami nasarar kashe yahudawan a cikin yankin. Shingayen tsaro wadanda suka kakkafa ko ta ina a yankin yamma da kogin Jordan basa basa amfa kamar yadda suke so, amma yahudawan sun kasa tabbatar da tsaron yahudawa yan share wuri zauna da ma jami’an tsaronsu da suke aiki a yankin.
Masana suna ganin idan HKI ta ci gaba da ayyukan soje masu tsanani a yankin mai yuwa su gamu da boren intifada na ukku a yankin, wanda kuma zai yi masu wuyar shawokansa.
Kafin haka dai ministan harkokin wajen HKI Isra’ila Katz ya bukaci a kori dukkan Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan, zuwa kasar Jordan.