Bangaren watsa labaru na kungiyar Hizbullah Lebanon ta fitar da bayani a jiya Lahadi da a ciki ta yi watsi da zargin da ma’aikatar harkokin cikin gida a Damascuss ta yi ma ta na cewa, tana gudanar da wasu ayyuka na ta’addancin a cikin kasar.
Bayanin na Hizbullah ya kunshi cewa; Hizbullah ba ta da wasu ayyuka ko wata alaka da wani bangare a cikin kasar ta Syria, tana mai bayyana zargin na ma’aikatar harkokin cikin gida da cewa, ba ta da tushe.
A jiya Lahadi ne dai ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta syrai riya cewa, ta kama gungun wasu mutane da suke ayyukan ta’addanci da suke da alaka da Hizbullah ta Lebanon.
Hizbullah ta ce; Ko kadan ba ta da wasu mutane acikin kasar ta Syria,ko alaka da wasu mutane a cikin kasar, abinda take fata shi ne ci gaba da zaman Syria a matsayin dunkulalliyar kasa mai tsaro da aminci.