Hizbullah Ta Yi Watsi Da Zargin Kasar Syria Akan Alaka Da Wata Kungiya Mai Makamai Da Aka Kama

A wani bayani da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar ta kore cewa tana da alaka da wata kungiya da ma'aikatar harkokin cikin gidan
Tambarin Hizbullah

A wani bayani da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar ta kore cewa tana da alaka da wata kungiya da ma’aikatar harkokin cikin gidan Syria ta kama mambobinta wacce kuma ta ce tana da alaka da Hizbullah din.

Bayanin na Hizbullah ya kara da cewa;Tana yi wa kasar Syria da al’ummarta fatan alheri da zaman lafiya, tare da yin kira ga mahukuntan kasar da su fadaka akan duk wani kokari na haddasa fitina a tsakanin Lebanon da Syria.

Bugu da kari Hizbullah ta yi kira ga gwamnatin kasar ta Syria da ta bi diddigin wadanda suke kokarin hadddasa wannan irin fitina a tsakanin kasashen biyu wanda ba kowa ba ne, sai makiya “Isra’ila da yake ci gaba da kai hare-hare a cikin kasashen Syria da Lebanon.

Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnatin Syria take zargin cewa ta gano wasu kungiyoyi a cikin kasar masu alaka da Hizbullah ta Lebanon. Kungiyar ta Hizbullah dai ta sha kore irin wannan zargin da ake yi mata, tana mai cewa ba ta da wata kungiya ko wani gungun mutane  da a cikin kasar.

Watanni kadan da su ka gabata ne dai Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa; zai gayyaci Sojojin Syria da su shiga cikin Lebanon domin su yi fada da kungiyar Hizbullah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted