A wani bayani da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta bayyana alhininta na shahadar babban hafsan mayakan rundunar “Kassam” ta kungiyar Hamas Muhammad Dhaif tare da wasu abokan aikinsa, tare da bayyana rawar da suka taka a fagen gwagwarmaya.
Kungiyar ta Hizbullaha ta mika sakon ta’aziyya da kuma barka akan shhadar Muhammad Dhaif ga kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas da sauran kungiyoyin Falasdinawa da kuma al’ummar Falasdinu. Haka nan kuma kungiyar ta Hizbullah ta mika sakon ta’aziyyar ga iyalan shahidan.
Kungiyar gwgawarmayar musuluncin ta Lebanon ta kuma ambaci cewa, Muhammad Dhaif ya tafiyar da dukkanin rayuwarsa ne wajen fada da ‘yan sahayoniya da kwankwasar kansu, musamman ma dai a yayin farmakin Aksa, da ya kasance daya daga cikin fitattun wadanda su ka shriya shi.