A jiya Asabar ne dai kungiyar ta Hizbullah ta fitar da sanarwa wacce a cikinta ta kira yi mazaun sansanonin ‘yan share wuri zauna na yahudawa 25 da su gaggauta tattara ya nasu, ya nasu su fice, saboda sojojin mamaya sun mayar da su sansanonin soja.
Sanarwar ta kuma ce; dukkanin wadannan sansanonin, sun zama wurin da za a rika kai wa hari, saboda daga nan ne ake kai wa Lebanon hare-hare.
Daga cikin wadannan sansanonin da akwai garuruwa kamar sun Haifa, Nahariya,Dabariyya da Akka.
A farkon watan Oktoba ma dai kungiyar ta Hizbullah ta gargadi ‘yan share wuri zauna a wasu sansanonin da su nesanci matsugunensu da sojoji su ka mayar wurin kai wa Lebanon hare-hare.
A wasu rahotanni da suke fitowa daga HKI sun ambaci cewa wani jirgin sama maras matuki da Hizbullah ta harba, ya sauka akan wata masana’anta ta kera makamai a garin Akka.
Majiyar ‘yan sahayoniyar ta kara da cewa, jirgin ya yi barna a jikin ginin masana’antar, sannan kuma ya jikkata mutane biyu.