Hizbullah Ta Gabatar Da Sakon Taya Murna Ga Pezeshkiyan Zabebben Shugaban Kasar Iran

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya mika sakon taya murna ga zabebben shugaban kasar Iran Masa’ud Pezeshkiyan saboda zabensa a matsayin

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya mika sakon taya murna ga zabebben shugaban kasar Iran Masa’ud Pezeshkiyan saboda zabensa a matsayin shugaban kasar Iran a zabe zagaye na 2 da aka gudanar a ranar jumma’an da ta gabata.

Tashar talabijan ta Almanar ta kungiyar Hizbullah ta nakalto Sayyid Nasarallah shugaban kungiyar yana fadar haka a rubutaccen sakon da ya aikewa zabebbeb  shugaban kasar ta Iran, ya kuma sha alwashin cewa kungiyarsa zata ci gaba da gwagwarmaya kan hanyar yaki da HKI har zuwa nasara tare da shugaban.

Mutane kimani miliyon 16 ne suka kada kuri’insu  a zaben shugaban kasa zagaye na biyu a ranar 5 ga watan Yulin  da muke ciki. Sannan Masa’ud Pezeskiya ya lashe zaben tare da kuri’u fiye da miliyon 16 na kuriu miliyon 30 da aka kada. Sannan abokin hamayyarsa Sa’id Jalili ya sami kuri’u miliyon 13 da yan kai daga cikinsu.

Daga karshe shugaban kungiyar ta Hizbullah ya kamala da cewa kungiyarsa da kuma na wasu kasashe a yankin suna yakar HKI da kuma babbar kawarta Amurka tun fiye da watanni 9 da suka gabata, kuma suna kallon Iran a matsayin babban mataimakiya a wannan fagen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments