Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi tir da hare-haren da HKI takai kan Wadi –Faraa a lardin Bikaa ta Arewa na kasar Lebanon inda ta kai hare-hare har kan rijiyoyin ruwa na mutane kasashen Syriya da Lebanon da suke lardin. Hare-haren sun kai ga shahadar mutane 12 da kuma daruruwan da suka ji rauni.
Tashar talabijin ta Al-manar ta nakalto majiyar kungiyar na fadar haka, ya kuma kara da cewa wadan nan hare-re suna da hatsari, don da alamun gwamnatin kasar Amurka wacce ta dauki hakkin kula da tsagaiuta budewa juna wuta wanda aka cimma da HKI ta mika mata ragamar al-amura na tayi duk abinda taga dama.
A danyan bangaren kuma inji bayanin, jami’an gwamnatin kasar Lebanon basa magana kwata-kwata a kan wannan al-amarin. Amma kungiyar da kuma mutane kasar Lebanon ba abinda wannan yake kara masu sai karfin guiwa da kuma tabbata kan abinda suka yi Imani da shi.