Hezbollah ta zafafa hare-harenta a kan yankunan Tel Aviv da  Haifa

Hezbollah ta sanar a yau Talata  cewa ta kaddamar da jerin hare-hare da mayakanta suka kai kan sojojin mamamya na Haramtacciyar Kasar Isra’ila, domin nuna

Hezbollah ta sanar a yau Talata  cewa ta kaddamar da jerin hare-hare da mayakanta suka kai kan sojojin mamamya na Haramtacciyar Kasar Isra’ila, domin nuna goyon baya ga al’ummar Palastinawa masu tsayin daka a zirin Gaza da kuma goyon bayan gwagwarmayar da suke yi, da kuma kare kasar Labanon daga hare-haren Isra’ila.

Harin na kungiyar Hizbullah wani bangare ne na dakarun Khaybar, wani bangare na mayakan kungiyar, wanda suke dakile yunkurin yunkurin sojojin Isra’ila na kutsawa garuruwa da kauyukan kudancin Lebanon.

Tun da sanyin safiyar yau, an yi ta jin karar  jiragen sama marasa matuka na Hizbullah a yankuna da dama, da suka hada da Haifa, Haifa Bay, Akka, da kuma gabashin Tel Aviv, a cewar dan rahoton tashar Al Mayadeen.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun ba da rahoton jin karar fashewar wasu abuwa masu karfin gaske a yankuna da dama na yankin tsakiyar Falastinu da yahudawa suka mamaye, tare da yin la’akari da cewa wani makami mai linzami ya kai hari a kudancin Beit Aryeh, kusa da Ramallah.

Haka nan kuma kafofin yada labaran Isra’ila sun ba da rahoton tasirin wani makami mai linzami da aka harba a yankin arewacin Caesarea, inda yahudawa da dama suka samu raunuka sakamakon harin.

A gefe guda kuma, hukumomin mamaya na Isra’ila sun bukaci mazauna wasu matsuguni a yammacin al-Jalil da su ci gaba da kasancewa a kusa da ramuka da aka gina domin tsira da rayukansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments