Pezeshkian : Duk wani harin da Isra’ila za ta kai wa Iran zai fuskanci Martanin da ya dace

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi gargadin cewa duk wani harin da Isra’ila za ta kai wa kasar zai fuskanci martanin da ya dace. Shugaban ya bayyana hakan ne yau yayin wata ziyara a ofishin kungiyar Hamas da ke birnin Tehran, inda ya karrama Yahya Sinwar shugaban kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa, wanda ya yi shahada […]
Shugabanin Kasashe Mambobin BRICS Na Isa Rasha Domin Halartar taron Kungiyar Karo Na 16

Shugabannnin kasashe mambobin BRICS, na isa kasar Rasha domin halartar taron kungiyar karo na 16 a binrin Kazan. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya isa birnin na Kazan na kasar domin halartar taron. A ranar Laraba ne shugaba Pezeshkian zai gabatar da jawabi a babban taron kasashen BRICS, wanda zai hada shugabannin kasashe mambobin BRICS. […]
Hezbollah Ta Dauki Alhakin Kai Harin jirgi Maras Matuki Kan gidan Netanyahu

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta ce ita ce ta kai harin jirgi maras matuki kan gidan shakatawa na firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a makon da ya gabata, kamar yadda jami’in hulda da yada labarai na Hizbullah Muhammad Afif, Mohammed Afif ya bayyana. Jami’in ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka […]
Araghchi: Iran na da nata hanyoyin na kare tashoshinta na nukiliya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya gargadi gwamnatin sahyoniyawa game da yin duk wani gigi na yin shsihigi a kan tashoshin nukiliyarta, yana mai jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dogara ne da kayan aikin soja na cikin gida da kuma hanyoyin da za ta kare kanta daga duk wani yunkurin wuce […]
Hezbollah ta zafafa hare-harenta a kan yankunan Tel Aviv da Haifa

Hezbollah ta sanar a yau Talata cewa ta kaddamar da jerin hare-hare da mayakanta suka kai kan sojojin mamamya na Haramtacciyar Kasar Isra’ila, domin nuna goyon baya ga al’ummar Palastinawa masu tsayin daka a zirin Gaza da kuma goyon bayan gwagwarmayar da suke yi, da kuma kare kasar Labanon daga hare-haren Isra’ila. Harin na kungiyar […]
Kais Saied : Tunisia na goyon bayan gwagwarmayar al’ummomin Falastinu da Lebanon

Shugaban kasar Tunusiya Kais Saied ya tabbatar a wannan Talata cewa kasarsa na tare da gwagwarmaya da tsayin daka na al’ummar Palasdinu da Lebanon, yana mai jaddada cewa mu’amala da ‘yan mamaya babban cin amana ne ga Falasdinawa. Saeed ya bayyana a cikin jawabin nasa cewa: “Muna tare da dukkanin al’ummomin da ake zalunta, mun […]
Matatar Mai Ta Dangote Ta Janye Karar Da Ta Maka NNPCL

Kamfanin Matatar Man Dangote ta ce za ta janye ƙarar da ta shigar na neman diyyar Naira biliyan 100 daga hukumar kula da kasuwancin man fetur kan dambarwar shigo da man fetur Najeriya daga ƙasashen waje. Matatar Dangote ta shigar ƙarar ne kan lasisin da hukumar ta bai wa kamfanin Matrix Petroleum Services na shigo […]
Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Fifita Shirin Zaman Lafiya A Yankin Gabas Ta Tsakiya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Babban fifikonta shi ne samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Bagha’ei ya jaddada cewa: Babban fifikon Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya shi ne samar da […]
Harin Wuce Gona Da Irin Sojojin ‘Yan Sahayoniyya Ya Lashe Rayukan Falasdinawa 10

Falasdinawa akalla 10 ne suka yi shahada wasu 30 kuma suka samu raunuka a harin da sojojin mamaya suka kai kan wata makaranta a sansanin Jabaliya Falasdinawa 10 ne suka yi shahada, wasu 30 kuma suka jikkata, a jiya Litinin, sakamakon luguden wuta da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi a kan makarantar share fage […]
Sojojin Yahudawan Sun Sake Aiwatar Da Kisan Kiyashi A Yankin Zirin Gaza

Sojojin yahudawan sahayoniyya sun gudanar da wani sabon kisan kiyashi a yankin Gaza ta hanyar kaddamar da hare-haren wuce gona da iri Rahotonni sun bayyana cewa: Fararen hula da dama da suka hada da kananan yara ne suka yi shahada tare da jikkata wani adadi mai yawa na Falasdinawa a sabbin hare-haren wuce gona da […]
Kungiyar Jihadul-Islami Ta Karyata Kashe Babban Sakatarenta Da Wasu Kafafen Yada Labarai Ke Watsawa

Kungiyar Jihadul- Islami ta musanta kashe babban sakatarenta Ziyad al-Nakhalah a kasar Siriya Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Jihadul-Islami ta Falastinu ta yi kakkausar suka tare da musanta abin da wasu kafafen yada labaran makiya suka ruwaito game da kishe babban sakatarenta, Ziyad al-Nakhalah ta hanyar kai hari kan wata motar farar hula a birnin Damascus […]
Shugabannin Kasashen Somaliya Da Djibouti Sun Tattauna Shirin Kungiyar Tarayya Afirka Kan Somaliya

Shugabannin kasashen Somaliya da Djibouti sun tattauna kan makomar tawagar Tarayyar Afirka a Somaliya Shugaban kasar Djibouti Isma’il Omar Guelleh ya tattauna da takwaransa na Somaliya Hassan Sheikh Mohamud, game da rawar da dakarun Tarayyar Afirka ke takawa wajen samar da zaman lafiya a Somaliya, da kuma hanyoyin tabbatar da mika jagorancin wanzar da kwanciyar […]