Kungiyar Hizbullah ta sanar da shahadar jami’in hulda da manema labarai na kungiyar Muhammad Afif al-Nabulsi, biyo bayan wani hari da Isra’ila ta kai masa a jiya.
A yammacin jiya Lahadi kungiyar Hizbullah ta tabbatar da cewa, jami’in hulda da manema labarai Hajj Muhammad Afif al-Nabulsi, ya yi shahada ne a harin wuce gona da iri da Isra’ila ta kai a yankin Ras Al-Naba a birnin Beirut, bayan shafe tsawon shekaru yana gudanar da aikinsa a fagen yada labarai na kungiyar.
Bayanin na kungiyar Hizbullah ya kara da cewa, duk da irin barazanar da Isra’ila ta shafe tsawon lokaci tana yi masa sakamakon yadda yake fitowa fili yana bayani kan ayyukan ta’addancinta, hakan bai tsorata shi ba.
Ya kasance mai jajircewa wajen isar da sakon gaskiya ga dukkanin al’ummomin duniya ba tare da tsoro ba, babban misalign hakan shi ne yadda yakan fito ya jagoranci tarukan manema labarai tare da bayyana matsayar kungiyar Hizbullah a kan batutuwa da dama da suka faru da kuma suke faruwa a yakin da ake yi da yahudawan sahyuniya, ko kuma hare-haren ta’addancinsua kan fararen hula da kaddarorin jama’a da na gwamnati a Lebanon.