Hare-Haren Wuce Gona Da Irin Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa

Hare-haren wuce gona da irin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Gaza tun daga safiyar yau, sun yi sanadiyyar shahadan Falasdinawa da dama tare

Hare-haren wuce gona da irin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Gaza tun daga safiyar yau, sun yi sanadiyyar shahadan Falasdinawa da dama tare da jikkatan wasu na daban

Rahotonni sun bayyana cewa: Fararen hulan Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu na daban tun daga wayewar garin ranar yau Talata, sakamakon luguden wuta da jiragen saman yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi kan yankuna daban-daban na zirin Gaza.

Shafin yanar gizo na Palestine Today ya nakalto daga majiyoyin lafiya na cewa: A kalla Falasdinawa 10 ne suka yi shahada sannan wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan makarantar Musa bin Nusair da ke dauke da ‘yan gudun hijira a unguwar Al-Daraj da ke tsakiyar birnin Gaza.

Wasu 15 na daban kuma sun yi shahada a lokacin da jiragen yakin sojin mamayar Isra’ila suka kai hari kan gidan mai na Radi a yammacin sansanin Nuseirat da ke tsakiyar zirin Gaza.


Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments