Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra\ila Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa A Zirin Gaza

Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-hare a yankuna daban-daban na Gaza, kuma Falasdinawa da dama sun yi shahada Jiragen yakin gwamnatin haramtacciyar

Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-hare a yankuna daban-daban na Gaza, kuma Falasdinawa da dama sun yi shahada

Jiragen yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun ci gaba da ruwan bama-bamai a yankuna daban-daban na zirin Gaza a rana ta 117 da yakin ya yi sanadiyar shahadan Falasdinawa da dama.

A cewar majiyoyin kiwon lafiya, sama da Falasdinawa 45 suka yi shahada tun daga wayewar garin Juma’a a zuwa safiyar yau a yankuna daban-daban na zirin Gaza.

Yousuf Al-Zaq, wanda aka bayyana shi a matsayin fursuna mafi ƙanƙanta bayan mamayar da aka kai wa gidansa da ke kan titin Al-Thawra a tsakiyar Gaza ya yi shahada.

An haifi Yousuf a cikin gidan yarin Isra’ila a shekara ta 2008, kuma sunansa yana da nasaba da labarin mahaifiyarsa, ‘yar fursuna Fatima Al-Zaq, wacce ta haife shi a gidan kurkuku.

Fararen hula 4 ne suka yi shahada yayin da wasu goma suka jikkata sakamakon harin bam da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida da ke kan titin Jaffa a unguwar Tuffah da ke gabashin birnin Gaza.

Kanun labarai

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted