Wasu Falasdinawa 16 ne suka yi shahada a wasu sabbin kisan gilla guda biyu da sojojin mamayar Isra’ila suka aiwatar a garin Jabaliya da birnin Gaza
Rahotonni sun bayyana cewa: Akalla Falasdinawa 16 da suka hada da kananan yara da mata ne suka yi shahada a yammacin jiya Laraba, a wasu sabbin hare-haren kisan kiyashi guda biyu da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai ta hanyar jefa bama-bamai a wasu gidaje biyu a garin Jabaliya da birnin Gaza.
Shafin sadarwa na yanar gizo na Wafa cewa: Akalla Falasdinawa 10 ne suka yi shahada, yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon harin da jirgin saman yakin ‘yan mamaya ya kai kan gidan iyalan Al-Najjar a garin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza.
Har ila yau, an bayyana cewa: Wasu Falasdinawa 6 sun yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon luguden bama-bamai da jiragen saman yakin sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida na iyalan Al-Zaytuuniya da ke kusa da makarantar Al-Ta’bi’een da ke unguwar Al-Daraj a gabashin birnin Gaza.
Sannan majiyoyin lafiya sun rawaito cewa: Wani jirgin saman leken asiri na Isra’ila ya harba bama-bamai a kofar asibitin Shahidi Kamal Adwan da ke arewacin Zirin Gaza.