Da safiyar yau Asabar sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun ci gaba da fadada wuraren suke kai wa hare-hare a zirin Gaza. Rahotannin da suke fitowa daga Gaza, suna nuni da cewa sojojin mamayar sun kai jerin hare-hare a gabashin birnin Gaza, da kuma a gabashin Deir-Balah, haka nan kuma a sansanin ‘yan hijira na Buraij a tsakiyar Gaza.
Rahotannin sun kuma ambaci cewa motoyin yakin sojojin mamayar sun kutsa gabashin Deir-Balah suna bude wuta da karfi a kusa da shigen da ya raba yankin gida biyu.
A gefe daya, jaridar “Haaretz” ta buga wasu hotuna na tauraron dan’adama da suke nuni da yadda sojojin mamayar suke kara kutsawa cikin yankin na Gaza da kara mamaye yankuna.
Shi kuma ministan yakin Isra’ila Yesra’il Kats cewa ya yi, sojojin nasu suna ci gaba da rusa abinda ya saura na yankin Gaza.
Ya zuwa yanzu dai sojojin mamaya sun rusa muhimman cibiyoyin da sun kai 2,500 daga lokacin da aka tsayar da yaki.
A jiya juma’a dai Falasdinawa 31 sun yi shahada daga cikinsu da akwai kananan yara biyu. A ranar Larabar da ta gabata ne dai manzon musamman na Amurka a yankin yammacin Asiya, Steve Witkkof ya sanar da cewa za a shiga mataki na biyu na tsagaita wutar yaki. A karkashin wannan matakin ne Amurkan take riya cewa za a kwace makaman kungiyoyin gwgawarmaya na Palasdinu a Gaza. Jumillar Falasdinawan da su ka yi shahada tun daga 2023 sun kai 71,000 da 455, sai kuma wadanda su ka jikkata da sun kai 171, da 347.