Search
Close this search box.

Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tana Amfani Da Makamai Masu Guba Kan Falasdinawa

Rahotonni sun bankado yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take yin amfani da muggan makamai masu guba wajen kashe yaran Falasdinawa Rahotonni da kwararru suka bankado

Rahotonni sun bankado yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take yin amfani da muggan makamai masu guba wajen kashe yaran Falasdinawa

Rahotonni da kwararru suka bankado sun tabbatar da cewa: Gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila tana yin amfani da hanyoyi daban-daban wajen kashe al’ummar Falasdinu a Zirin Gaza, ciki har da amfani da muggan makamai masu guba da suke haddasa annoba da bullar cututtuka masu saurin kisa.

Wakilin gidan talabijin na Al-Alam a Al-Zawaida ya bayyana cewa: Kwararru sun gano cewa, ba wai kawai hare-haren rokoki ne suke kashe Falasdinawa a Gaza ba, a’a, har da shara da lalata kayayyakin more rayuwa da wani nau’in makami mai guba da ke kashe mutane ta hanyar haddasa musu munanan cututtuka da annoba kamar kwalara da cutar hanta.

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun hana hukumomi kwashe shara da datti zuwa yankunan gabashin Zirin Gaza, lamarin da ya tilastawa kananan hukumomin jigilar su zuwa yankin Al-Zawaida, wanda ke dauke da dimbin Falasdinawa ‘yan gudun hijira da suka rasa matsugunansu. Yayin da zubar da sharar a wuraren da su dace ba, warinta ke haifar da yaduwar cututtuka da janyo yawaitar sauro da kwari, baya ga muggan makamai masu guba da aka yi amfani da su kan gidaje da haimomin ‘yan gudun hijira.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments