Hamas Ta Yi Watsi Da Barazanar Amurka Da Isra’ila Kan Musayar Fursunoni

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da barazanar da Isra’ila da Amurka ke yi kan batun musayar fursunoni. Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da barazanar da Isra’ila da Amurka ke yi kan batun musayar fursunoni.

Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya fada cewa Isra’ila tana kaucewa aiwatar da wasu tanade-tanade na yarjejeniyar tsagaita bude wuta,” yana mai gargadin cewa ba za a sako mutanen da ake garkuwa da su ba idan ba Isra’ila ta mutunta yarjejeniyar ba.

Qassem ya ce, “Matsayinmu a fili yake, kuma ba za mu amince da barazanar Amurka da Isra’ila ba,” in ji Qassem, bayan firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya yi barazanar komwa yaki idan har ba a sako mutanen da aka kama ba zuwa ranar Asabar.

A ranar Laraba, ministan harkokin soji na gwamnatin ya yi gargadin cewa Isra’ila za ta sake fara yakin Gaza idan Hamas ta gaza sakin ‘yan Isra’ila da take tsare da su kuma a wannan karon za ta yi barna.

“Sabon yakin na Gaza zai sha bamban kuma mai tsanani da wanda ya gabata kafin tsagaita bude wuta, kuma ba zai kare ba sai mun fatattaki Hamas da kuma sako dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su,” in ji Isra’ila Katz a cikin wata sanarwa.

“Hakan kuma zai ba da damar tabbatar shirin shugaban Amurka Donald Trump game da Gaza,” in ji Katz, yayin da yake magana kan shirin shugaban Amurka na mamaye yankin Falasdinu.

A baya dai kungiyar Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, wata tawaga karkashin jagorancin babban mai shiga tsakani ta isa birnin Alkahira inda ta fara ganawa da jami’an Masar” suna sa ido kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments