Sanarwar da kungiyar ta kungiyar Hamas ta fitar ta ce; Harin dabbanci da ‘yan share zauna da kuma sojojin mamaya akan kauyen Talfit dake kudancin Nabulus da sauran yankuna da dama a yammacin kogin Jordan, wanda ya hada da rushe gidaje da dukiyoyin mutane, da kuka jefa tsoro da razani a cikin Falasdinawa, haka nan kuma bude musu wuta kai tsaye da ya jikkata mutane da dama, wani Karin laifi ne da ayyukan ta’addanci da hukumar ‘yan sahayoniya take tsarawa.
A wani bayani da kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta fitar, ya bayyana cewa; Gwamantin Netanyahu wacce mai laifi ne ta fito da wani salon fadan kare dangi ga al’ummar Falasdinu.
Haka nan kuma sanarwar ta kungiyar ta Hamas ta ci gaba da cewa; Abinda ya faru share fage ne na aiwatar da kai wasu hare-haren a cikin sauran kauyuka da garuruwa da kuma sansanonin Falasdinawa a yammacin kogin Jordan.
Kungiyar ta gwgawarmaya ta Falasdinawa ta kuma yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da MDD kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa da kungiyar kasashen musulunci da su fito su yi tir da laifukan ‘yan mamaya a yammacin Korgin Jordan, sannan kuma da daukar matakain da za su hana aiwatar da gina matsugunan ‘yan share wuri zauna.
Haka nan kuma kungiyar ta Hamas ta kira yi mutanen yankin yammacin Kogin Jordan da dukkanin kungiyoyin siyasa da su hada karfi wuri daya, domin fuskantar wannan bakar siyasar. Haka nan kuma Hamas ta bukaci ganin an yi gwgawarmaya da dukkanin fuskokinta da jaddada hakkin falasdinawa na kawo karshen mamaya da kafa Daular Falasdinawa mai babban birnin a Kudus.