Hamas Ta Yi Kira Da A Hanzarta Daukan Matakin Ceto Hukumar Bada Agajin Falasdinawa Ta UNRWA

Bayan Allah wadai da ƙasashen duniya suka yi, Hamas ta yi kira da a ɗauki matakin gaggawa don ceto hukumar UNRWA Kungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta

Bayan Allah wadai da ƙasashen duniya suka yi, Hamas ta yi kira da a ɗauki matakin gaggawa don ceto hukumar UNRWA

Kungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta (Hamas) ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa bayan Allah wadai da kasashen Turai tara, Kanada, da Japan suka yi kan harin da Isra’ila ta kai wa Hukumar UNRWA. Hamas ta jaddada bukatar tabbatar da ci gaba da samar da tallafin jin kai ga Falasdinawa ba tare da wani cikas ba, ganin yadda matakan da Isra’ila ke dauka kan ofisoshinta da ma’aikatanta ke kara ta’azzara.

Wannan kira ya zo ne bayan tsananta yakin da Isra’ila ke yi da hukumar ta UNRWA, wanda ya hada da takaita ayyukanta da kuma kai hari ga ofisoshinta da ma’aikatanta a Kudus da Zirin Gaza.

Hamas ta jaddada cewa miliyoyin Falasdinawa sun dogara ne da ayyukan agaji, ilimi, da kiwon lafiya na Hukumar UNRWA, wanda hakan ya sanya kariyar ayyukanta ya zama muhimmin batu dangane da tabarbarewar rikicin jin kai.

A cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta Hamas ta bukaci wadannan kasashe da su mayar da matsayinsu da aka ayyana zuwa matakai na zahiri don matsa lamba ga gwamnatin mamayar Isra’ila, tare da tabbatar da dawo da ayyukan agaji na Hukumar UNRWA ba tare da wani cikas ba, ganin yadda bala’in jin kai da al’ummar Falasdinawa ke fuskanta ke kara ta’azzara, sakamakon munanan manufofin gwamntin mamayar Isra’ila. Kungiyar Hamas ta kuma yi kira ga sauran kasashen duniya da su dauki irin wannan matsayi don yin Allah wadai da halayen gwamnatin mamayar Isra’ila tare da matsa mata lamba ta dakatar da ayyukanta da kuma cin zarafin da take yi wa Hukumar UNRWA, da kuma ba ta damar gudanar da ayyukan jin kai bisa ga umarnin Majalisar Dinkin Duniya, ba tare da wani takunkumi ko kuma yin barazana ga siyasa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted