Hamas Ta Yi Gargadi Akan Yadda ‘Yan Sahayoniya Suke Son Mayar Da Masallacin Kudus Na Yahudawa

Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta fitar da wani bayani wanda ya kunshi yin gargadi akan yadda ‘yan sahayoniya suke kokarin mayar da masallacin Kudus

Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta fitar da wani bayani wanda ya kunshi yin gargadi akan yadda ‘yan sahayoniya suke kokarin mayar da masallacin Kudus na yahudawa, tare da yin kira ga al’ummar Musulmi da su dauki matakan da su ka dace domin dakatar da wannan Shirin mai hatsari.

Cibiyar Watsa labaru ta Falasdinawa ta nakalto kungiyar ta Hamas tana yi Allawadai da yadda ‘yan mamaya su ka kama limamin masallacin Kudus Sheikh Muhammad Ali Al-Ababsi, da kuma kokarin nesanta shi daga Masallacin Kudus da hana shi ci gaba da limanci.

Kungiyar ta Hamas ta bayyana abinda ‘yan sahayoniyar suke yi da cewa tsoma baki ne a cikin harkoki tafiyar masallacin na Kudus wanda ba zai zama karbabbce ba.

Haka nan kuma kungiyar ta “Hamas” ta ce; yadda ‘yan mamaya suke keta hurumin masallacin kudus, da sanyawa masu zuwa salla cikinsa sharudda da ka’idoji, da kutsen da ‘yan share wuri zauna suke yi a cikinsa, dukkanin wadannan matakai ne na share fage da suke yi, domin mayar da masallacin na yahudawa.

Bugu da kari sanarwar ta Hamas ta yi Ishara da wani Shirin na  ‘yan sahayoniyar dake son raba masallacin gida biyu a tsakaninsu da musulmi ko kuwa ware lokacin da yahudawa ne kadai za su shiga ciki su  yi salon bautarsu a ciki.

Wani sashe na bayanin kungiyar ta “Hamas” ya kunshi kira ga al’ummar Falasdinu da su yi ribadi a cikin masallacin na Kudus domin ba shi kariya. Haka nan kuma ta yi kira ga kungiyar kasashen larabawa da ta musulmi da gwamnatoci da al’ummun musulmi a ko’ina a duniya da su yi yunkura da gaggawa domin kai wa masallacin na Kudus dauki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted