Hamas Ta Ce  Za Ta Amince Da Yarjejeniyar Da Za Ta Biya Bukatun Al’ummar Falastinu

Shugaban ofishin siyasa na kungiyar, Ismail Haniyeh ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba. Ya ƙididdige buƙatun ƙungiyar a matsayin “dakatar da

Shugaban ofishin siyasa na kungiyar, Ismail Haniyeh ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba.

Ya ƙididdige buƙatun ƙungiyar a matsayin “dakatar da kisan kiyashi da ta’addancin Isra’ila, da janyewar sojojinta gaba ɗaya daga Gaza, da musayar fursunoni.”

Da yake karin haske kan jawabin nasa, Haniyeh ya ce, “Kungiyar Hamas tana gudanar da shawarwarin ne dauke da wannan matsayi, wanda ke wakiltar muradin al’ummarmu da kuma gwagwarmayarsu.”

Shugaban na Hamas ya yi nuni da wani tattaki da yahudawa masu tsatsauran ra’ayi suka yi a jiya Laraba, inda dubban yahudawan ‘yan share wuri zauna suka kutsa cikin harabar masallacin quds mai alfarma tare da keta alfarmarsa.

Yahudawa sun udanar da tattakin ne a daidai lokacin da suke  gudanar da jerin gwano da suke kira ranar tuta mai cike da cece-kuce, wanda ke nuni da kawo karshen yakin kwanaki shida da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi da wasu kasashen larabawa a shekara ta 1967, wanda ya kai ga mamaye yankin Falasdinawa ba bisa ka’ida ba, ciki har da Gabashin birnin  Kudus.

Gwamnatin Isra’ila tana daukar dukkan al-Quds, a matsayin babban birninta, duk kuwa da cewa bisa dokar majalisar Dinkin duniya gabashin birnin Quds mallakin Falastinawa ne.

Haniyeh ya ce: kutsen na yahudawa a masallacin Quds, ya tabbatar da cewa mamayar Quds it ace babban burin yahudawan, wanda kuma Falastinawa basu taba ja da baya wajen gwagwarmayar kare wannan wuri mai tsarki ba, in ji Haniyeh.

A farkon watan Mayu, Hamas ta amince da wani kudurin sasantawa da ke ba da damar dakatar da wuce gona da iri da kuma sakin sauran mutanen da aka kama, amma gwamnatin yahudawan Isra’ila, ta yi watsi da shawarar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments