Hamas Ta Ce Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Isra’ila Ya Nuna Gazawar Tsarin Duniya Na Dakatar Da Ita.

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar Hamas ta fadi cewa fashewar bama-bama da rushewar gidaje da mutuwar mutane da dama a daidai lokacin da ake tsananin

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar Hamas ta fadi cewa fashewar bama-bama da rushewar gidaje da mutuwar mutane da dama a daidai lokacin da ake tsananin ruwan sama da sanyi a yankin gaza ya kara tabbatar da kisan kiyashi isra’ila kan alummar Gaza, kuma ya kara tabbatar da gazawar tsarin duniya na daukar mataki don dakatar da ita.

Hamas ta ce isra’ila ce ke da alhakin duk wani bala’i da ake ciki a gaza, kuma ta soki kasashen duniya na yi gum da baki game da abubuwan dake faruwa ,don haka tana kira da a dauki matakin gaggawa domin janye killacewar da Isra’ila ta yi wa yankin don bada dama a shigar da kayayyakin agaji da kuma fara sake gina yankin.

Hazem Qassem kakakin kungiyar Hamas ya jaddada cewa ci gaba da rushewar gidaje da isra’ila ta rusa a hare-haren baya bayan nan yana kara nuna irin bala’in da falasdinawa ke ciki a yankin na rashin isar kayan agaji, don haka yayi kira da a dauki matakin gaggawa don dakatar da hare-haren, a fara sake gina yankin da samar da matsugunne da suka dace ga alummar Gaza

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted