Hamas Ta Bayyana Rushe-Rushen Gidajen Falasdinawa Wanda HKI Ta YI A Qudus, Korar Falasdinawa daga Kasarsu Ne Ta Wata Hanyar

Kungiyar Hamas mai gwagwarmaya da HKI a kasar Falasdinu da aka mamaye, ta bayyana cewa rushe-rudhen gidajen da gwamnatin HKI take yi wata hanya ce

Kungiyar Hamas mai gwagwarmaya da HKI a kasar Falasdinu da aka mamaye, ta bayyana cewa rushe-rudhen gidajen da gwamnatin HKI take yi wata hanya ce ta korar Falasdinawa daga kasarsu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana fadar haka a wani bayanin da ta fidar a yau Talata. Ta kuma kasar da cewa shirin yahudawan na rusha gine-ginen falasdinawa kama daga gidaje da wuraren aiki ko gonaki, yana nufin korasu daga kasarsu ne, don haka dole ne Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan su tashi tsaye don ganin cewa sun dakatar da hakan ko kuma sun rage shi.

A cikin yan kwanakin da suka gabata ne gwamnatin HKI ta rusa gidajen falasdinawa 13 a garin Anata dake gabacin birnin Qudus, wanda ya tilastawa falasdinawa a yankin zama yan gudun hijira.

Daga karshen kungiyar ta bukaci kungiyar kasashen larabawa da kuma kungiyar kasashen musulmi su dauki matakan da suka dace don hana yahudawan ci gaba da rusa gine-ginen Falasdinwa, musamman a birnin Qudus.

Har’ila yau hukumar OCHA ta MDD ta bada sanarwan cewa HKI ra rusa gidajen Falasdinawa 1,787 a yankin yamma da kogin Jordan kadai, daga ranar 7 ga watan octoban shekara ta 2023 zuwa 15 ga watan Octoban shekara ta 2024. Daga ciki har da gidajen  Falasdinawa 800.

Kuma rushe-rushen sun shafi gine-ginen  Falasdinawa 4,498, sannan wasu Falasdinawa 532000 rushewar ta shafa, kama daga gidajen zama, gonaki da shaguna ko wuraren sana’arsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments