Wani Jami’in kungiyar Hamas ya bada sanarwan cewa a farfado da tattaunawa don kawo karshen yaki a Gaza.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Basem Na’im, wani jami\in kungiyar yana fadawa kamfanin dillancin labaran Associated Press kan cewa, an shiga wata sabuwar tattaunawa tsakanin wakilan kungiyar Hamas da kuma na HKI don kawo karshen yakin da ke faruwa a Gaza kimani watanni 14 da suka gabata.
Na’im ya ce an gabatar masu da wata takarda ta shirin kawo karshen yakin, amma kungiyar Hamas tana kan ginshikan al-amura da take kansu a tattaunawar baya, wadanda suka hada da dakatar da yaki na din din din, da kuma ficewar HKI daga zirin Gaza.
Na’im yace kungiyar tana iya sassuci a lokacin ficewar sosojin HKI daga gaza, amma batun ficewa dole ne.
Kafin haka dai, a tattaunawar baya, HKI ta bukaci ta wanzar da sojojinta a Gaza, bayan dakatar da wuta, a yankin da ake kira ‘Philidepia’ dake kan iyaka da kasar Masar da kuma ‘Nitsarim’ wanda yake tsakiyar Gaza, ya kuma raba yankin arewa da kudancin yankin na gaza. Na’im ya kara da cewa akwai fatan za’a sami nasara a tattaunawar na yanzu, saboda shugaban kasar Amurka mai zuwa, yana da ra’ayin kawo karshen yake-yake a yankin gabas ta tsakiya.