Hadakar Kasashen Sahel Alliance, Na Shirin Kafa Rundinar Hadin Guiwa Mai Dakaru 5,000 

Hadakar kasashen nan uku na yankin Sahel AES da ta hada Burkina Faso da Mali da Nijar na shirin kafa wata rundunar soji ta hadin

Hadakar kasashen nan uku na yankin Sahel AES da ta hada Burkina Faso da Mali da Nijar na shirin kafa wata rundunar soji ta hadin gwiwa mai dakaru 5,000.

Ministan Tsaron Nijar Janar Salifou Modi ne ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa da gidan talabijin na kasar RTN a ranar Talata.

Ministan ya bayyana cewa sabuwar rundunar wadda ta kunshi sojojin kasa da na sama da kuma na tattara bayanan sirri na dab da fara aiki domin dakile barazanar tsaro a yankin na Sahel.

Janar Modi ya ce shugabannin sojojin kasashen uku sun kammala duk wani shiri da ya dace kuma nan da makonni kadan rundunar zata fara aiki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments