Habasha ta yi alkawarin ci gaba da yaki da “Al-Shabaab” ta  Somaliya

Habasha ta bayyana cewa “kokarin da take yi na raunana kungiyar Al-Shabaab zai ci gaba, domin tabbatar da cewa an kawon karshen barazanar da kungiyar

Habasha ta bayyana cewa “kokarin da take yi na raunana kungiyar Al-Shabaab zai ci gaba, domin tabbatar da cewa an kawon karshen barazanar da kungiyar take yi ga tsaron kasashen yankin.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Habasha, Nebiat Getachew, ya ce, “Al-Shabaab za ta ci gaba da zama tushen damuwa ga tsaron kasarmu, kuma za a ci gaba da fuskantar ta a kowane hali don hana ta zama barazana ko barin wata kafa ta sake bullarta a wasu bangarori na yankin. ”

“Idan aka yi la’akari da cewa Habasha da Somaliya makwabta ne da ba za a iya raba su ba, Habasha za ta ci gaba da aiwatar da dabarunta ta hanyar da za ta inganta hadin gwiwar yankin a cikin dogon lokaci,” in ji shi.

Bayanin ma’aikatar harkokin wajen Habasha ya zo ne bayan sanarwar da ministan tsaron Somaliya Abdikadir Mohamed Nur ya bayar a ranar Asabar cewa “Ethiopia ba za ta shiga cikin tawagar Tarayyar Afirka da za ta tallafa wa Somaliya ba,” tawagar da ke shirin fara aikinta a watan Janairun 2025.

A cikin wata sanarwa da ya aikewa gidan talabijin na kasar ya bayyana cewa, “yarjejeniya ta baya-bayan nan tsakanin Habasha da Somaliland ta jefa ‘yanci da cin gashin kai da ma hadin kan kasar Somaliya cikin hadari.”

Dangantakar diflomasiyya tsakanin Habasha da Somaliya ta yi tsami ne sakamakon yarjejeniyar  hadin gwiwa da aka rattaba hannu a kanta tsakanin Habasha da Somaliland a ranar 1 ga Janairu 2024, domin hakan ya saukaka wa Habasha kaiwa zuwa teku cikin sauki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments