Sojojin gwamnatin kasar Habasha sun kwace garin adwa na yankin Tigray kuma kusa da kan iyaka da kasar Eriuteria ba tare da sun gamu da wata turjiya ba, saboda mayakan TPLF sun fice daga garin.
Shafin yanar gizo na labarai africanews ya bayyana cewa, sojojin sun sami wannan ci gaban ne a dai dai lokacinda ake tada jijiyoyin wuya tsakanin kasashen biyu, sai dai duk da haka al-amura suna kara komawa kamar yanda suke a lardin na Tigray. Daga cikin an dawo da zirga zirgan jiragen sama tsakanin Adisababa da kuma birnin Mekelle babban birnin lardin.
Yan kabilan Tigray ne suka mamaye madafun iko a kasar Habasha kafin shekara ta 2018 a lokacinda Aby Ahmed ya zama firay ministan kasar. Ahmad dai ya fito ne daga yankin Oromia ya kuma sami nasarar dai dait wasu daga cikin al-amuran da mutanen Tagray suka lalata a kasar.
Amma wannan ya jawo yakin basasa nay an shekaru kafin a sulhunta sai dai a wannan shekara ta 2026 sun sake yankin tawaye wanda a wannan karon ma gwamnatin Ahmed ya sami nasara a kansu. Mayakan Tigray dai sun samun goyon bayan wasu kasashen yankin inda suke boyewa su kuma kawo hare hare a cikin kasar.