Hukumar lafiya ta duniya ta bada sanarwan cewa har yanzun ana ci gaba da aman wuta a kan dutsen Dofan da ke arewacin laradinoromia na kasar Habasha.
Gwamnatin kasar Habasha ta bada sanarwan cewa ya zuwa yanzu ta tsugunar da mutanen fiye da dubu 80 nesa da inda aka yi girgizan kasa a yau a tsakiyar kasar.
Tashar talabijan ta VOA ta bada labarinn cewa tun ranar 2 ga watan Jenerun da muke ciki ne wurin ya fara fidda hayaki da iska mai zafi da kuma ruwa a kan utsen Dofan na tsakiyar kasar ta Habasha.
A yau Laraba kuma an yi girgizan kasa mai karfin ma’aunrin richta 5.5 a yankin, kuma wannan shi ne biyu a cikin wannan watan.