Gwamnatin Sudan ta yi maraba da shawarar Sanya muggan laifukan Dakarun kai daukin gaggawa a matsayin “kisan kare dangi” kan al’ummar kasar
Gwamnatin Sudan ta yi marhabin da matakin da Majalisar Dokokin Amurka ta dauka na Sanya muggan laifuffukan Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces a Darfur a matsayin kisan kare dangi.
Ministan harkokin wajen Sudan Ali Youssef Al-Sharif ya bayyana a shafinsa na twitter a dandalin “X” cewa ya yi maraba da kuduri mai lamba 1328 na majalisar wakilan Amurka, wanda ya bayyana laifukan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da mayakan sa-kai da suke kawance da su a Darfur da suka aikata a matsayin laifukan kisan kare dangi. Majalisar Wakilan Amurka baki daya ta amince da wani kudurin da ya bayyana abin da kungiyar ‘yan tawayen Rapid Support Forces da kawayenta suka yi a yankin Darfur a kan kabilun da ba na Larabawa ba a matsayin kisan kiyashi da cin zarafin bil adama, a cewar daftarin kudurin da wakilin jam’iyyar Republican John James ya gabatar a ranar 27 ga watan Yuni na shekara ta 2024, a ƙarƙashin lamba 1228.