Gwamnatin jamhuriya Nijar ta yi watsi da zargin sace makamashin Uranuim da aka jibge a cibiyar Somair da ke arwacin kasar da kamfanin Orano mallakin Faransa ya yi mata.
Gwamnatin Nijar , ta bakin ministocinta na shari’a dana ma’adinan karkashin kasa,a taron ministocin da suka kira a ranar asabar, ta jaddada aniyarta na tabbatar da cikakken ‘yanci kan makamashinta na Uranuim.
Wanan takaddamar na zuwa ne mako guda bayan da bangaren shari’ar Faransa ya kaddamar da bincike akan abin da ya kira da shiryayya sata domin cimma muradin wata kasa.
Tun bayan juyin mulkin shekara 2023 da sojoji su kayi kasar, kamfanin Orano ya shiga takun-saka da sabbin mahukuntan na Nijar kan batun ma’adinin Uranuim da Allah ya fuwacewa kasar .
A watan Yunin wanan shekarar, shugabanin sojan Nijar suka karbe kamfanin Somair inda aka jiye sama da Tannes dubu 1 na karfin Uranuim tare da mayar dashi na gida.