Mabiya mazhabar Durus na kasar Siriya a yau Alhamis sun yi musayar fursunoni da gwamnatin kasar Siriya.
Tashar talabijan ta Al-Mayadeen tv ta kasar Lebanon ta bayyana cewa hukumar ‘salib Ahmar’ ta kasa da kasa ce take shiga tsakani a wannan musayar wanda ya hada da mabiya mazhabar durus 61 da kuma sojojin gwamnatin kasar Siriya 25 wadanda suke tsare a hannun a yankin Suwaida na kudu maso gabacin kasar.
A wani labarin kuma majiyar gwamnatin yankin Suwaida na kudancin kasar ta Siriya ta bada sanarwan musayar fursunonin wanda za’a yi a birnin Suwaida. Sanarwar ta kara da cewa wannan shi ne karon farko wanda ake musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu tun bayan yakin da suka fafata tsakaninsu a cikin ranin da ya gabata wanda ya kai ga rasa rayukan mutane da dama.