Gwamnatin kasar Paraguaya ta tsige shugaban kasa Santiago Pena daga kan kujerar shugabancin kasar, sannan ta tsareshi saboda zamaba cikin amince da dama da yayi sanadiyyar hana mutanen kasar miliyon 3 kaiwa da ajiyarsu a wani bankin kasar.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto kafafen yana labaran kasar na cewa a ranar Alhamis da ta gabata ce Pena ya sauka daga kujerar shugabancin kasar, bayan gagarumar zanga zangar da mutanen kasar suka gudanar, sannan a jiya Jumma’a majalisar dattawar kasar ta tsige shi, sannan ta kuma yi masa daurin talala a wani gida, har’ila yau ta dauke masa gurkuwan gurfana a gaban kuliya wanda tsoffin shuwagabbin kasar suke da shi. Pene dai abokin shugaba Trump na Amurka, da kuma Firay ministan HKI benyanmin Natanyahu ne. Ya yi amfani da matsayinsa na siyasa a kasar ya bawa kansa bashin kudade a bankin Ueno na kasar, wanda ya hana masu asusun kudade a bankin kaiwa ga kudadensu. Tuni dai majalisar ta rantsar da mataimakinsa Pedro Alliana a matsayin shugaban kasa, har zuwa lokacinda wa’adinsu zai kare ashekara ta 2028.