Hukumar Kare Hakkin masu sayen kayayyakin more rayuwa ta Tarayya (FCCPC) ta bai wa ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a fannin kasuwanci wa’adin wata daya da su sauke farashin kayayyaki.
Sabon shugaban hukumar FCCPC da aka nada Tunji Bello, ya bayyana haka a wani taron kwana daya da masu ruwa da tsaki suka yi kan hauhawar farashin kayayyaki a ranar Alhamis a Abuja.
Cikin sanarwar da ya bayyana a ranar Alhamis a Abuja, Bello ya ce hukumar za ta fara aiki bayan cikar wa’adin.
Ya ce taron an yi shi ne don magance ƙaruwar hauhawar farashin kayayyakin masarufi da kuma mugun hali na ƙungiyoyin ‘yan kasuwa.
Bello ya yi bayanin yadda Hukumar ta gano cewa ana siyar da injin markaɗa kayan marmari da aka fi sani da Ninja a wani babban kanti da ke Texas akan dala $89 kwatankwacin Naira dubu ɗari 140, amma an baje wannan samfurin akan kuɗi Naira dubu 944, da ɗari 9 da 99.00 a wani babban kanti da ke Victoria Island a Legas.
Bello ya yi mamakin dalilin tashin farashin gwauron zabin da ake amu ba bisa ƙa’ida ba idan aka kwatanta da lamarin a Jihar Texas ta Amurka.
Ya ce ƙaruwar farashin da ba su dace ba, da suka haɗa da ƙayyade farashin na yin barazana ga zaman lafiyar tattalin arzikin ƙasar.
“A ƙarƙashin sashe na 155, masu karya dokar ko dai ɗaiɗaikun mutane ko kamfanoni na iya fuskantar hukunci mai tsanani da suka haɗa da tara da ɗauri idan kotu ta same su da laifin.