Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) na shirin sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya a ranar Laraba, 14 ga watan Janairu, domin karfafa zaman lafiyar aiki da inganta yanayin koyar da karatu a jami’o’in Nijeriya. Wannan na kunshe ne cikin wata gayyata a hukumance da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta fitar, inda ta gayyaci shugabannin jami’o’in tarayya domin halartar bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a Abuja.
Sabuwar yarjejeniyar ta kuma kunshi sabon tsarin tallafin kudade ga jami’o’i, inda za a ware kudi na musamman domin bincike, da dakunan karatu, da dakunan gwaje-gwaje, da kayan aiki da bunkasa kwarewar ma’aikata.
Ma’aikatar Ilimin ta bayyana yarjejeniyar a matsayin wani babban ci gaba a tattaunawar da aka dade ana yi tsakanin gwamnati da ASUU, tare da nuni da cewa hakan na nuna kudirin gwamnati na tabbatar da zaman lafiya a fannin ilimi.
An cimma yarjejeniyar ne a ranar 23 ga Disamba, 2025, bayan kammala sake tattauna yarjejeniyar 2009 tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU, lamarin da ya kawo karshen takaddamar da aka shafe sama da shekaru 16.