Search
Close this search box.

Gwamnatin Masar Ta Yi Tir Da Munanan Halin Fira Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Gwamnatin Masar ta yi dirar mikiya kan munanan manufofin fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu Gwamnatin Masar ta dorawa fira ministan gwamnatin haramtacciyar

Gwamnatin Masar ta yi dirar mikiya kan munanan manufofin fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu

Gwamnatin Masar ta dorawa fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu sakamakon alhakin zafafan kalamansa dangane da yankin Philadelphia tare da zarginsa da kokarin kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza da yarjejeniyar musayar fursunoni da kuma kawo cikas ga shiga tsakanin Masar da Qatar da kuma Amurka.

Ma’aikatar harkokin wajen Masar a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Talata ta ce: Gwamnatin Masar ta yi watsi da kalaman fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke kara ruruta wutar rikici a yankin, tare da dorawa gwamnatin Isra’ila sakamakon alhakin irin wadannan kalamai da ke kara dagula al’amura da nufin ci gaba da wanzuwar ayyukan ta’addanci da manufofin tada hankali.

Sanarwar ta kara da cewa: Gwamnatin Masar ta kuma yi watsi da yunkurin Netanyahu na yin amfani da sunan Masar wajen kawo cikas ga cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni a zirin Gaza.

Sanarwar ta kuma jaddada aniyar Masar ta ci gaba da taka rawar da ta taka mai dimbin tarihi wajen jagorantar shirin samar da zaman lafiya a yankin, wanda zai kai ga tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kuma kwanciyar hankali ga daukacin al’ummomin yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments