Muhammad Al-Huthi, mamba a kwamitin siyasa na kasar Yamen ya bayyana cewa, kasarsa a shirye take ta fuskanci duk wani irin hare-haren da za’a kawo wa kasar daga waje, musamman bayan barazanar da HKI da magoya bayanta suka yi a baya-bayan nan.
Kamfanin dillancin labaran Sahab na kasar Iran, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Parstoday, yana cewa: Gwamnatin kasar Yemen ta shiryawa duk hare-haren da makiya za su kawo mata a cikin kasar.
Muhammad Al-Huthi ya kara da cewa, Amurka da Burtaniya da kuma kawayensu suna tsammanin sun rage karfin kawancen masu gwagwarmaya da su ke yankin Asiya, tare da abubuwan da suka faru a Lebanon da kuma Siriya. Amma idan sun sake kawowa kasar hare-hare za su fahinci cewa ba haka bane.
A ranar Asabar da ta gabata ce, sojojin Yemen suka kai hari da makami mai linzami samfurin balistik a kan yankin ‘Yafa da ke Arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye, tare da haddasa asarori masu yuwa.