Gwamnatin Kasar Bangladesh Ta Kafa Dokar Hana Fita Da Kawo Karshen Zanga Zanga

Hukumomi a kasar Bangladesh sun kafa dokar hana fita a babban birnin kasar Daka, saboda kawo karshen zanga zangar da aka dauki kwanaki ana gudanarwa

Hukumomi a kasar Bangladesh sun kafa dokar hana fita a babban birnin kasar Daka, saboda kawo karshen zanga zangar da aka dauki kwanaki ana gudanarwa a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kafafen yada labaran kasar Bangladesh na cewa a cikin yan kwanakin da suka gabata rikicin da ake yi ya kai ga an fasa wani gidan yari a babban birnin kasar wanda ya kai ga tserewar fursinoni da dama. Banda haka rikicin ya lakube rayukan mutane akalla 67 ya zuwa yanzu.

Labarin ya kara da cewa rikicin ya tashi ne sanadiyyar dokan da gwamnatin kasar ta kafa wacce ta ware mukamai masu muhimmanci a kasar don dangin shugaban day a jagoranci kasar zuwa yencin kai a shekara 1971.

Kakakin gwamnatin kasar Naeemul Islam Khan ya bayyana cewa zasu tura sojojin don dawo da zama lafiyan a kasarm musamman a birnin Dakar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments