Gwamnatin Iran Tana Kan Bakanta Na Kammala Aikin Layin Dogo Mai Suna ‘Mashigar Arewa-Kudu’

A lokacin ganawarsa da mataimakin firay ministan kasar Rasha, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta kammala, shirin shimfida

A lokacin ganawarsa da mataimakin firay ministan kasar Rasha, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta kammala, shirin shimfida layin dogo wanda ake kira (North-South corridor) wanda zai hada kasashen turai musamman kasar Rasha da kasashen Asiya, bayan sun ratsa cikin kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka ne a jiya litinin a ganawarsa ta Vitaly Saviev mataimakin firay ministan kasar Rasah.

Ya kuma kara da cewa aiwatar da shirin shimfida layin dogo daga Rasht zuwa Astana shirin ne wanda kasashen Rasha da Iran suka kulla yarjeniya a kansa, wacce ake kira FIMA. Kuma Iran a shirye take ta aiwatar da abinda ya haw kanta na aiwatar da shirin, sannan za ta taimakawa kasar Rasha da dukkan ayyukan samar da takardun da take bukata don aiwatar da nata bangaren, na yarjeniyar ko shirin.

A nashi bangaren mataimakin Firay ministan kasar Rasha Vitaly Saview ya ce idan shirin layin doga na Rasht-Astana ya kammala kasashen biyu zasu iya musayar kayaki wadanda zasu kai ton miliyon  15 a ko wace shekara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments