Search
Close this search box.

Gwamnatin Falasdinu ta bukaci Kwamitin Sulhu na MDD da ya kakaba takunkumi a kan Isra’ila

Gwamnatin Falastinu ta bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar da ya sanya wa Isra’ila takunkumi a daidai lokacin da take ci gaba da kashe fararen hula

Gwamnatin Falastinu ta bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar da ya sanya wa Isra’ila takunkumi a daidai lokacin da take ci gaba da kashe fararen hula a duk fadin Gaza da ta yi wa kawanya.

”Isra’ila na ci gaba da kashe rayukan mutane tare da ɗaukar duk wani mataki da ka iya rura wutar rikicin yankin Gabas ta Tsakiya, a daidai lokacin da muke gudanar da taron cika shekaru 75 na yarjejeniyar Geneva,” in ji Mansour a wani taron gaggawa na kwamitin sulhu da Aljeriya ta buƙaci a gudanar bayan Isra’ila ta kai wani mumunan hari ta sama a wata makaranta da Falasdinawa ke samun mafaka.

“Bari na fayyace muku hali da ake ciki, Isra’ila ba ta damu da sukar ku ba.. ta yi watsi da kuɗurorinku, ba ta jin muhawar da ku,” in ji Mansour, yayin da yake nuni kan wakilin Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya Gilad Erdan.

Da yake kira ga mambobin kwamitin da kar su yi watsi da aikinsu su kuma yi amfani da duk damarmakin da suke da su don aiwatar da matakai, jakadan Falasɗinu ya tambayi cewa: Sai yaushe ne za a kama gwamnatin Isra’ila da laifukan da take aikatawa?

Ya bukaci cewa “lokaci ya yi da za a sanya takunkumi” ga Isra’ilawa da ke da alhakin aikata laifukan yaƙi kuma ya ce: “Yaushe ne za ku aiwatar da shawararku da dokokin kasa da kasa? Kuna buƙatar sanya takunkumi a kan waɗannan masu laifi.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments