Ministan harkokin cikin gida na Syria ya shaidawa gidan talabijin na kasar cewa jami’an tsaro sun kafa wani shinge a kusa da Damascus yayin da mayakan ‘yan adawa ke cewa suna kutsawa cikin babban birnin kasar.
Mohammed al-Rahmoun ya ce “Akwai wani shingen tsaro mai karfi da sojoji sukayi wa Damascus da yankunanta, kuma babu wanda zai iya kutsawa cikin wannan layin na tsaro da sojoji sukayi,”
A wani labarin kuma ofishin shugaba Bashar al-Assad ya musanta rahotanni da ke cewa ya tsere daga Damascus, babban birnin kasar, a daidai lokacin da gungun ‘yan adawan kasar masu dauke da makamai ke ci gaba da dannawa kan hanyar zuwa babban birnin da kuma Aleppo.
Ofishin ya yi Alla-wadai da “labaran karya da ake yada wa”, inda ya kara da cewa shugaban na ci gaba da gudanar da ayyukansa daga Damascus din.