Gaza : Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Za Ta Fara Aiki A Karfe 06:30 Agogon GMT Lahadi Inji Qatar

Kasar Qatar ta sanar da cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a baya-bayan nan tsakanin gwamnatin Isra’ila da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas

Kasar Qatar ta sanar da cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a baya-bayan nan tsakanin gwamnatin Isra’ila da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas za ta fara aiki da safiyar Lahadi daga karfe 06:30 agogon GMT.  

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar Majed al-Ansari ya sanar da cewa, “Kamar yadda bangarorin da ke cikin yarjejeniyar da masu shiga tsakani suka shirya tsagaita bude wuta a zirin Gaza, za a fara tsagaita bude wuta a zirin Gaza da karfe 8:30 na safe a ranar Lahadi 19 ga watan Janairu, agogon kasar.”

Kakakin ya kuma bukaci mazauna Gaza da su yi taka tsantsan da jiran umarnin hukuma.

Khalil al-Hayya mataimakin shugaban hukumar siyasa ta Hamas, ya yabawa al’ummar Gaza bisa nasarar da suka samu a yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 15 ana yi na kisan kare dangi a kan yankin da aka yiwa kawanya.

Ya kara da cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta amince da yarjejeniyar bayan ta fuskanci daruruwan hare-haren ramuwar gayya daga kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments