Gaza: Yara Kanana Na Daga Cikin Mutane Kimani 40 Wadanda Sojojin HKI Suka Kashe A Yau Alhamis A Wata Makarantar MDD

Jiragen yakin HKI sun kai farmaki da makamai masu linzami kan wata makaranta ta MDD a yankin Nusairat na zirin Gaza, inda Falasdinwa yan gudun

Jiragen yakin HKI sun kai farmaki da makamai masu linzami kan wata makaranta ta MDD a yankin Nusairat na zirin Gaza, inda Falasdinwa yan gudun hijira suke samun mafaka a cikinta. Akalla falasdinawa 40 ne suka yi shahada 5 daga cikinsu yara kanana ne a wannan harin.

Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto Isma’ila Athawabiti darektan watsa labarai na gwamnatin Gaza, yana fadar haka, ya kuma kara da cewa akwai yiyuwar yawan wadanda suka rasa rayukansu su karu saboda akwai wadanda suke cikin mummunan hali da aka kaisu wasu wurare don taimakon jami’an jinya da likitoci.

Gwamnatin HKI ta tabbatar da wannan labarin ta kuma kara da cewa ta kai hare hare da jiragen sama da kuma makaman masu igwa a kan makarantar ta hukumar UNRWS ne don mayakan Falasdinawa suna samun mafaka a cikinta.

Athawabit ya karyata zancen gwamnatin yahudawan, ya kuma kara da cewa, bay au ne  HKI ta saba fadin karya irin wannan ba, don bawa kanta uzurain aikata irin wanna kissan kiyashin. Kafin haka MDD ta bada sanarwan cewa falasdinawa kimani miliyon guda suna iya mutuwa saboda yunwa a gaza a cikin watan Yuli mai zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments