A sabbin hare haren da sojojin HKI suka kai kan sansanin yan gudun hijira ta ‘Al-Jadid” kusa da Nusairaat a zirin Gaza falasdinawa 6 ne suka yi shahada.
Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEW ya bayyana cewa banda falasdinawa 6 da suka yi shahada, wasu 72 sun yi rauni.
Majiyar ta nakalto ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta kara da cewa a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata falasdinawa 89 sojojin HKI suka kai ga shahada a duk fadin zirin gaza.
Ya zuwa yanzu dai tun bayan fara yaki a Gaza, a ranar 7 ga watan Octoban da ya gabata, sojojin HKI sun kai falasdinawa 33,634 sannan dubu 76,216 ne suka jikata.
A wani labarin kuma wasu labaran a gaza sun bayyana cewa sojojin HKI sun kai farmakikan gungun yan jarida a zirin na gaza wanda ya kai ga jikatar da dama daga cikinsu, wasu daga cikinsu sai an yake gabbansu.