Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da shahadar wasu falasdinawa 5 sanadiyyar ci gaba da hare-haren sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila da hakan ya sa jumillar adadin shahidai ya kai 72,382,sai kuma wasu 175,416 da su ka jikkata.
An sami wadannan shahidan 5 ne a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata, yayin da wasu 18 kuma su ka jikkata.
Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ta kuma ce tun daga tsagaita wutar yaki a ranar 11 ga watan Oktoba, 2025 zuwa yanzu wadanda su ka yi shahada sun kai 1,493, sai kuma wadanda su ka jikkata da sun kai 5,299. Haka nan kuma a wannan tsakanin an fito da shahidai 836 daga karkashin baraguzai.
Haramtacciyar kasar ta Isra’ila tana ci gaba da kai hare-hare ta sama da kasa da jirage marasa matuki a sassa mabanbanta na Gaza.