Rahotanni daga Gaza na cewa dukkan sisbitocin birnin Rafah sun daina aiki sakamakon hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa yankin ba kakkautawa.
Tun daga farkon watan Mayun nan Mutane miliyan guda ne suka riga suka fice daga yankin, dake kudancin zirin Gaza, wanda ya kasance wurin da ake ci gwabza fada.
MDD, ta bayyana halin da ake ciki da babban bala’in jin kai, a yankin, da ya zama wata ”Jahannaba a doron Kasa”
A halin da ake ciki dai ma’aikatar lafiya ta Hamas ta sanar a jiya Laraba, cewa mutane 36,171 ne sukayi shahada a zirin Gaza tun bayan fara yakin fiye da watanni bakwai da suka gabata.
Akalla mutane 75 ne aka kashe a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, in ji sanarwar da ma’aikatar ta fitar, inda ta kara da cewa mutane 81,420 ne suka jikkata tun ranar 7 ga watan Oktoba.