Gaza : Adadin Falasdinawan Da Sukayi Shahadi Tun Ranar 7 Ga Watan Oktoban 2023 Ya Zarce 47,000

Akalla Falasdinawa 47,035 ne aka kashe yayin da 111,091 suka jikkata a harin da sojojin Isra’ila suka kai a Gaza tun ranar 7 ga Oktoban

Akalla Falasdinawa 47,035 ne aka kashe yayin da 111,091 suka jikkata a harin da sojojin Isra’ila suka kai a Gaza tun ranar 7 ga Oktoban 2023, in ji ma’aikatar lafiya ta Falasdinu da ke Gaza a ranar Litinin.

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu da ke da hedkwata a Gaza ta ce a cikin sa’o’i 24 da suka gabata an kashe mutane 60 tare da gano wasu gawarwakin mutane 62.

A cikin sanarwar da ma’aikatar Falasdinawan ta fitar ta ce, an samu nasarar kwato shahidai 122 da suka hada da gawarwakin mutane 62, yayin da wasu 341 da suka jikkata suka isa asibitocin zirin Gaza a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

Yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas ta fara aiki ne a safiyar Lahadi da karfe 08:30 agogon GMT.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments