Rahotanni sun bayyana cewa gamayyar jam’iyun siyasa a kasar Iraqi sun gudanar da taron gaggawa domin tattaunawa kan harin hadin guiwa da Amurka da Saudiya su kai a kasar , inda suka bayyana harin a matsayin keta hurmin kasar, kuma barazana ne ga zaman lafiya da tsaron yankin.
har ila yau sun bayyana cewa wadannan hare-haren ba zu taimaka ba a kokarin da ake yi na daidaita lamaru, za su kara dagula alamura ne da kuma kara jefa yankin cikin rikici da rashin zaman lafiya da tsaro a fadin yankin baki daya,
gamayyar jam’iyun sun bayyana cewa bai kamata gwamnati da jam’ian tsaron kasar iraqi su amince da wannan wuce gona da iri din ba, ko kuma tabasu ta kowanne yanayi ,kuma sun yi watsi da duk wai kokari na mayar da kasar ta zama filin dagan gwada kwanji na yankin da ma na duniya
a jiya laraba dakarun kungiyar Hashdu shaabi ta sanar da shahadar mayakanta guda 20 tare da jikkata wasu 32 a harin ta’addanci da Amurka da kasar Saudiya suka kai akan sansanoni daban daban na kungiyar a larduna daban daban a kasar Iraqi, da suka hada da nainawa, basara, karkuk,karabala diyala
kungiyar ta ce babu makawa za ta mayar da martani mai tsanani kan wannan harin da aka kai mata